Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da asusun UNICEF sun yi Kira ga gwamnatocin duniya da su cigaba da wayar da kan al’umma game da mahimmancin shayar da jarirai nono uwa zalla na tsawon akalla watanni shida bayan haihuwa.
Shugabanin sun ce yin haka zai taimaka wajen ceto rayukan yara sama da 820,000 dake mutuwa duk shekara a duniya.
Likitoci sun bayyana shayar da jariri nono uwa zalla musamman na tsawon watanni shida ko ma fiye da hakan don fa’idar sa wajen kara lafiyar jarirai.
A cikin shirin FA’IDAR NONON UWA za mu ji yanda za a kore rashin fahimtar shayar da jarirai nonon uwa zalla.
Sunana Aisha Mohammed da zan gabatar .