Daga
Bamanga Abdullahi Gombi
Majalisar Masarautar Huba da ke Jihar Adamawa ta sanar da nadin Hakimai bakwai na dindin domin cike guraben da babu Hakimai a masarautar.
Nadin ya biyo bayan amincewar Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri.
A cikin wata sanarwa da Ke failed da Sa Gannon Sakataren Majalisar Masarautar, Alhaji Abba A. Sale ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wasu jerin sunaye da Ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ta ce wadannan sunaye ba daga Majalisar suka fito ba.
Sanarwar ta shawarci jama’a da su dogara kawai ga sahihan bayanai da suka fito daga hukumomin da suka dace.
Sabbin Hakimai da aka nada su ne: ACG Andrew Barka (mai ritaya) Gundumar Kulinyi, Alhaji Mahmoud Abdulkadir Gundumar Shangui, Alhaji Abdulnasir Iya Abbas Gundumar Mufa, da Mr. Clifford N. Kadala Gundumar Uding.
Sauran su ne: Mr. Henry Kadiri Gundumar Hyama, Mr. Aliyu Ibrahim Gundumar Yadul, da kuma Mr. Anderson Tsowurda Gundumar Mugwahi.
Majalisar Masarautar ta Hoba ta taya sabbin Hakiman murna tare da yi musu fatan samun nasara da zaman lafiya a Gundumominsu.
Wannan nadi wani gagarumin mataki ne na karfafa mulkin a matakin kasa da kuma zurfafa tsarin gargajiya a fadin Masarautar Huba.
Majalisar ta kuma jaddada cikakkiyar goyon bayanta ga hangen nesa na jagorancin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da Tol Huba, Alheri Bulus Nyako, wajen samar da shugabanci na kowa da kowa, da kiyaye al’adun gargajiya, da kuma isar da dimokradiyya mai ma’ana ga al’umma.

